Ma’aikatan da suka fito daga daukacin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya, shugabanin kungiyar na kasa sun koka da cewa an maida kananan hukumomi ‘yan baya ga dangi a tsarin tafiyar da mulkin Najeriya, batun da suka ce lokaci yayi da yan Najeriya zasu ce basu amince ba.
Mr Emmanuel Fashe, dake zama sakataren yada laban kungiyar a Najeriya ya bayyana cewa sun gudanar da gangamin ne domin kwatowa kananan hukumomi ‘yan ci.
An dade ana batun 'yancin kananan hukumomin Najeriya. Duk da yake kawo yanzu majalisar wakilai ta amince da bukatar, to amma akwai jan aiki a gaba kafin amincewar ta zama doka ganin cewa a majalisun baya an yi irin wannan yunkurin na yin gyaran domin baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kansu.
Kwamarad Ibrahim Khalil, shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, NULGE, shine ya jagoranci tattakin da ma’aikatan suka yi har zuwa majalisar dokokin jihar Taraba.
Wannan ma ko na zuwa ne yayin da a Najeriya wasu jihohin kasar ke kasa biyan ma’aikatan kananan hukumomi albashi, ciki har da jihar Taraba mai masaukin baki, batun da shugaban kungiyar yace ba zasu lamunce ba.
Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum