Shugaban kungiyar Shehu Sheni yace ganin yadda sabon nauin cutar ke hallaka mutane da dama a Najeriya musamman a arewacin kasar lokaci yayi da zasu hada kai da gwamnati domin samar da allurar rigakafi.
A cewarsa suna hada kai da mahukumta domin a shigo da allurar saboda ba'a yinta a Najeriya.
Akan cewa lokaci yayi da su masana kimiyar ya kamata su soma sarafa allurar cikin gida, shugaban kungiyar ya yadda lokaci yayi su soma duba cikin gida da zummar hada magungunan.
Kwamishanan lafiya na jihar Dr. Kuden Kamshak yace mutane uku ne ake harsashen sun kamu da kwayar cutar a jihar. Yace an kwantar dasu a Asibitin Filato inda aka yi masu jinya kafin a sallamesu. Kawo yanzu babu wanda cutar ta hallaka a jihar.
Inji kwamishanan suna cigaba da wayar da kawunan mutane akan cutar saboda haka mutane su guji cunkoson jama'a.
Shi ma daraktan tsaftace muhalli na jihar Christopher Ditai ya jaddada mahimmancin tsafta domin gujewa cutar da ma cututtuka masu saurin yaduwa musannan a lokacin zafi da kuma saukowar damina.
Yace a dinga tsaftace kasuwa da gidajen kwana da duk wuraren da jama'a ke yin anfani dasu.
Shi ma daraktan hukumar wayar da kawunan jama'a ta kasa dake jihar Filato Bulus Dabit yace suna cigaba da fadakar da jama'a ta hanyar amfani da sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum