A jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin yankin arewa maso gabas da suka sha fama da rikicin Boko Haram yawancin filaye da aka saba yin noma da can baya yanzu sun zama rairayi kawai saboda kwararowar hamada.
Bayan matsalar da kungiyar Boko Haram ta haddasa akwai kuma sare itatuwa da mutane su keyi domin samun makamashin dafa abinci. Mutane suna sare itatuwa babu ji babu gani walau domin yin aikin sassaka kotoci ko kuma samun abun dafa abinci.
Wasu gonakin da aka bari da kayukan da jama'a suka arce daga muhallansu domin harin 'yan ta'adan sun zama holoko domin baicin kashe mutane kungiyar ta Boko Haram ta kone kayuka da dama. Ta lalata gonakai ta kuma sare itatuwa domin yin anfani dasu wurin gine-gine
Ga bidiyon Sanusi Adamu da karin bayani
DOMIN KARIN BAYANI
Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci http://bit.ly/2kT7h6n
Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci http://bit.ly/2lujeAU
Facebook Forum