Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Zai Ba Da Lambar Yabo Ta Shugaban Kasa Ga Amurkawa 19


Mutanen 19 da suka fito daga rukuni daban-daban da shugaban Amurka Joe Biden ya karrama a ranar Juma'a saboda yin abin da Fadar White House ta kira a tsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen bada gudunmawa a bangarori daban-daban, da tsaron Amurka da wasu muhimman ayyuka ga al'umma.

Maza 10 da mata 9, daga rukuni daban-daban da suka hada da siyasa, wasanni, nishadi, ‘yan rajin kare ‘yancin jama'a da kungiyar LGBTQ+, kimiyya da addini.

Sanarwar daga Fadar White House ta ce "wadannan Amurkawa goma sha tara sun gina kungiyoyi, tare da hadin kan al’umma da kuma harkokin kasuwanci don inganta rayuwar Amurka da Amurkawa.

Bakwai daga cikin su 'yan siyasa ne da suka hada da tsohon magajin garin New York kuma mai bayar da agaji, Michael Bloomberg, dan majalisa James Clyburn, tsohuwar Sanata Elizabeth Dole, mai fafutukar sauyin yanayi kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Al Gore, tsohon wakilin Biden na sauyin yanayi John Kerry, tsohon Sanata Frank Lautenberg wanda ya rasu a shekarar 2013, sai kuma tsohuwar kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi.

Pelosi ita ce mace ta farko da ta taba zaba Kakakin Majalisar Wakilan Amurka.

Clarence B. Jones yana daga cikin wadanda za a karrama, Jones, mai shekaru 93, za a karrama shi ne saboda gudunmawar da ya bayar a lokacin fafutukar kare hakkin jama'a. Jones lauya ne wanda yake da shawarwari ga Martin Luther King Jr. kuma ya taimaka wajen rubuta jawabin Martin Luther King na "I Have Dream" wanda ya gabatar a watan Maris a shekarar 1963 a Washington.

Akwai kuma Medgar Evers zai samu lambar yabo bayan mutuwarsa ne saboda aikin da yayi sama da shekaru sittin da suka gabata wajen yaki da da nuna wariya ga bakaken fata a Mississippi a tsakanin shekarun 1960 zuwa 1963 a matsayin jami'i na farko a hukumar NAACP a jihar. Yana da shekaru 37 lokacin da aka harbe shi a gaban gidansa a watan Yunin 1963.

‘Yar wasan fina-finai, Michelle Yeoh, ta kafa tarihi a bara inda ta zama mace ‘yan Asiya ta farko da ta samu lambar yabo ta Academy Award saboda rawar da ta taka a cikin fim din “Everything, Everywhere All at Once.”

Jim Thorpe, wanda ya rasu a shekara ta 1953, shi ne Ba’amurke na farko da ya samu lambar zinare ta gasar Olympics.

Judy Shepard ita ce ta kafa gidauniyar Matthew Shepard, gidauniyar da ta ci sunan danta, dake Jami'ar Wyoming wanda ya mutu a shekarar 1998 bayan da aka daure shi a jikin wani shinge aka yi masa duka saboda dan Luwadi ne.

Sauran wadanda suka samu lambar yabo sune:

- Gregory Boyle, limamin da ya kafa cocin Jesuit Catholic inda yake taimakawa tare da kawo karshen harkar daba.

- Phil Donahue, dan jarida ne kuma tsohon mai gabatar da shirye-shiryen talabijin na rana.

- Katie Ledecky, 'yar wasan ninkaya data kafa tarihi.

- Opal Lee, mai fafutuka wanda aka fi sani wajen taimakawa aka kafa ranar hutu ta bakaken fata Amurkawa da aka fi sani da Juneteenth

- Ellen Ochoa, macen ta farko ‘yar Hispaniya da ta taba zuwa sararin samaniya kuma mace ta biyu a matsayin daraktar Cibiyar Sararin Samaniya ta NASA.

- Jane Rigby, masaniyar ilmin taurari wanda itace babbar masanin kimiyyar na'urar hangen nesa mafi karfi a duniya.

- Teresa Romero, shugabar kungiyar ma'aikatan gona ta United Farm Workers kuma mace ta farko ‘yar Hispaniya da ta jagoranci kungiyar ta kasa a Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG