Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Janye Wasu Dakarunta A Chadi


Sojojin Amurka
Sojojin Amurka

Amurka na shirin janye wasu dakarunta na wucin gadi daga kasar Chadi, a cewar jami'an Amurka a ranar Alhamis, matakin da ya zo kwanaki kadan bayan da Washington ta amince da janye sojojinta daga makwabciyarta Nijar.

WASHINGTON, D. C. - A farkon wannan watan ne babban hafsan sojin saman Chadi ya umarci Amurka da ta dakatar da ayyukan da ake yi a wani sansanin sojin sama da ke kusa da N'Djamena babban birnin kasar, kamar yadda wata wasika da aka aike wa gwamnatin rikon kwarya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Manjo Janar Patrick Ryder ya ce wani bangare na sojojin Amurka da ke Chadi za a janye su daga kasar.

Ya ce wannan mataki ne na wucin gadi, a wani bangare na nazarin hadin gwiwar tsaro da kasar Chadi, da za a koma bayan zaben shugaban kasar da za a yi a ranar 6 ga watan Mayu.

Wani jami’in Amurka da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce wasu dakaru goma sha biyu na musamman da ke kasar Chadi a matsayin masu tsare-tsare da masu ba da shawara za su koma Jamus a yanzu.

Shugaba Mahamat Idriss Deby mai rikon kwarya zai tsaya takara a watan gobe, abin da ya sa kasar Chadi ta zama ta farko a cikin kasashen yammacin Afirka da ke karkashin mulkin sojan kasar da suka shirya kada kuri'a.

Amma 'yan adawa sun nuna damuwa game da amincin sa.

Ya zuwa yanzu, babbar kasar da ke tsakiyar Afirka ta kasance babbar abokiyar kawance ga sojojin kasashen yammacin duniya da na shiyya-shiyya a yakin hadin gwiwa da masu ikirarin jihadi a yankin.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan wata 4 ga watan Afrilu ministan sojin kasar Chadi, babban hafsan hafsan sojin sama Idriss Amine Ahmed ya ce ya shaidawa jami’an tsaron Amurka da su dakatar da ayyukan Amurka a sansanin jiragen sama na Adji Kossei bayan “Amurkawa” sun kasa nuna shaidar takardu da ke tabbatar da kasancewarsu a kasar.

Faransa wacce ta yi mulkin mallaka har yanzu tana da sojoji 1,000 da jiragen yaki da ke da sansani a kasar Chadi.

Wannan dai ya zama babban jigon dabarun tsaro na yammacin Turai a yankin tun bayan da Nijar makwabciyarta ta kori sojojin Faransa bayan da sojojinta suka kwace mulki a wani juyin mulki a bara, biyo bayan irin wannan mataki da sojojin Mali da Burkina Faso suka dauka.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG