Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan California Sun Tarwatsa Sansanin Masu Zanga-zangar Goyon Bayan Falasdinu a Jami’ar UCLA


Masu Zanga-zangar Goyon Falasdinu A Jami'ar California
Masu Zanga-zangar Goyon Falasdinu A Jami'ar California

Daruruwan ‘yan sanda masu hular kwano ne suka kutsa da karfin tuwo zuwa tsakiyar wani filin taro a Jami’ar California a birnin Los Angeles da safiyar yau Alhamis domin wargaza sansanin da masu zanga zangar goyon bayan Falasdinawa suka kafa da magoya bayan Isra’ila suka kai musu hari cikin dare.

Samamen da ‘yan sandan suka kai da sanyin safiya a Jami’ar ta UCLA shine wuri na baya baya da ake samun tankiya a harabar jami’o’in Amurka, inda aka gudanar da zanga zangar kin amincewa da ayyukan Isra’ila a yaki da take yi a Gaza, wanda ya kai ga samun arangama tsakanin dalibai da ma jami’an tsaro

Wani hoton talbijin ya nuna an kama kimanin masu zanga zanga 6, sun rusuna a kasa, an daure hannayen su ta baya.

An ji karar abubuwan fashewa da dama yayin arangaman da wata na’ura mai kama da gurneti da ‘yan sandan suka harba domin tarwatsa su.

Wasu masu zanga-zangar, dake dauke da abubuwan kariya da laima, sun nemi hana jami’an kutsawa da dan karamin adadinsu, yayin da suke ta ihun cewa, “ku tura su baya” tare da haska fitilu masu haske a idanun ‘yan sandan. Wasu kuma da ke daura da sansanin sun karaya cikin sauri, an kuma gansu suna tafiya kana sun dora hannayensu a ka ’yan sanda na musu rakiya.

Da yammacin ranar Laraba, jami'ai a cikin dabara sun fara shiga cikin harabar jami’ar ta UCLA tare da jibge kansu a gefen sansanin da aka kafa da tantuna da gungun masu zanga-zangar suka mamaye, faifan bidiyon da aka nuna kai tsaye daga wurin ya bayyana haka.

Tashar talbijin na birnin KABC-TV ta kiyasta masu zanga zanga 300 zuwa 500 suka boye a cikin sansanin, yayin da kimanin wasu 2,000 suka taru a bayan shigaye suna bada goyon baya.

Amma ’yan sandan da suka hallara sun tsaya a gefen shingen na tsawon sa’o’i kafin daga bisani suka fara tirsasa hanyar shiga sansanin da misalin karfe 3:15 na safe PDT (1015 GMT), inda suka tarwatsa shingayen tare da kame mutanen da suka ki fita.

Wani gungun jami'an sintiri na babbar hanyar California ne ya jagoranci samamen dauke da garkuwa da sanduna.

Wasu masu goyon bayan Falasdinu sun ce an cillo musu wuta kana an lankada musu dan karen kashi da sanduna.

Jami'an jami'ar sun dora alhakin tarzomar akan "masu tayar da hankali" kana sun lashi takobin gudanar da bincike.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG