Shugaba Biden ya sanar da shirin ba da tallafin dala $770 sau daya ga wadanda gobarar daji ta shafa a California.
Wannan tallafin na a matsayin wani bangare na kokarin samar da agaji daga gwamnatin tarayya yayin da gobarar ke ci gaba da karuwa.
“Ba za mu jira sai bayan an shawo kan gobarar ba kafin mu fara taimaka wa wadanda abin ya shafa. Kamar yadda kowa ya sani. Wadanda wannan gobarar ta shafa za su sami tallafin kudi na dala $770 sau daya, domin su sayi abubuwa kamar ruwa, abincin jarirai, da magunguna da sauri,” in ji Biden yayin wani jawabi da ya yi game da gobarar dajin a ranar Litinin a Fadar White House.
Shugaban ya bayyana cewa kusan mutum 6,000 sun riga sun yi rijista don amfana da wannan shirin, kuma an riga an fitar da kudi na dala miliyan 5.1 kamar yadda jaridar The Hill ta yanar gizo ta ruwaito.
Hukumar ba da agajin gaggawa a matakin tayarra ta FEMA ta kaddamar da shirin tallafi da ake kira “Critical Needs Assistance Program” a makon da ya gabata, wanda ke bai wa wadanda suka tsira damar karbar wannan tallafin kudi na $770 sau daya, a cewar wani jami’in Fadar White House.
Dandalin Mu Tattauna