Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya gana da takwaransa na Angola Joao Lourenco a fadarsa dake birnin Luanda.
Ana sa ran Biden da Lourenco su tattauna akan batutuwan da suka shafi ciniki da zuba jari tsakanin kasashen 2, tare da yin tsokaci akan hanyar Lobito, ta gyara layin dogon da za’a rika amfani da shi wajen yin jigilar ma’adinai daga kasashen dake cikin nahiyar Afrika zuwa tashar ruwan angola ta lobito dake gabar tekun atlantic.
A cewar fadar White House, ziyarar Biden ta kasance irinta ta farko da wani shugaban Amurka mai ci ya taba kaiwa kasar Angola, kuma ita ce ziyarar farko da wani shugaban Amurka ya kai yankin kudu da saharar Afirka tun cikin shekarar 2015.
Biden yayi karin haske akan mahimmancin wannan ziyara mai cike da tarihi a jawabin daya gabatar a Luanda a yau Talata.
“Ina mai matukar alfahari da kasancewata sugaban amurka na farko daya ziyarci Angola, ina matukar alfahari da dukkanin abin da muka yi tare, domin sauya kawancenmu zuwa wannan mataki, akwai sauran aiki a gabanmu, akwai abubuwa da dama da zamu aiwatar.
Biden ya fayyace alkawarin gwamnatin Amurka ga kawancenta da Afirka.
“Amurka ba za ta gaji ba a kan Afirka. Ba za mu gaji ba a kan Afirka. Ina ganin tabbacin ikirarin da na yi, kun taba jina na fada a baya, amma Amurka ba za ta gaji ba a kan Angola. Gwamnati na kawai ta zuba jarin fiye da dala biliyan 3 a Angola kawo yanzu. Makomar duniya na nan a Afirka, a nan Angola. Don haka a wannan ziyara ina sa ran tattaunawa a kan yadda zamu tabbatar da mutane sun ci gajiyar tsarin dimokiradiyya.”
Biden zai kai ziyara tashar jirgin ruwa ta Lobito tare da ganawa da hukumomin hada-hadar kudi na Afrika, ciki har da wakilai daga kasashen Zambia da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo kafin ya bar Angola a gobe Laraba.
Dandalin Mu Tattauna