Mataimakin kwamishinan gundumar Aizawl Nazuk Kumar ya shaidawa AFP cewa, ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 12, "muna kuma neman karin wasu".
Babban daraktan 'yan sanda Anil Shukla ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na NDTV cewar ya zuwa yanzu ana samun cikas ga kokarin ceto a cikin ramin saboda ruwan saman.
Babban Ministan Mizoram Lalduhoma ya ba da diyya ga iyalan wadanda bala'in ya shafa sakamakon guguwar Remal.
Ofishin hukumar kula da yanayi a Indiya ya ba da gargadi game da mamakon ruwan sama a fadin Mizoram da sauran jihohin arewa maso gabas ranar Talata.
A jihar Assam mutum daya ya mutu sannan ruwan sama mai karfi ya katse wutar lantarki, in ji babban minista Himanta Biswa Sarma a wata sanarwa da ya fitar.
Guguwar ta afkawa kasar Bangaladesh da makwabciyarta India a yammacin Lahadin da ta gabata tare da kakkabo igiyoyin wutan lantarki.
Gabaɗaya, aƙalla mutane 38 ne suka mutu a cikin guguwar da ta tashi.
A Indiya, mutane takwas ne suka mutu a jihar Bengal ta Yamma, kamar yadda jami'ai suka fada a yau talata, inda suka sabunta adadin mutanen da suka rasa rayukansu, wanda ya kai adadin zuwa akalla 21.
A makwabciyar kasar Bangladesh, inda guguwar da ta fi karfi, akalla mutane 17 ne suka mutu, a cewar ofishin kula da bala’in da ‘yan sanda.
Dandalin Mu Tattauna