Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Shirin ‘Ba Sani Ba Sabo’ Don Yaki Da Rashawa a Jamhuriyar Nijar


Shugaban Kasar Nijar, Bazoum Mohamed.
Shugaban Kasar Nijar, Bazoum Mohamed.

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya kaddamar da farautar mahandama dukiyar jama’a a karkashin shirin da ake kira Operation ‘’Ba-sani Ba-sabo’’ inda tuni bincike ya rutsa da wani babban jami’i a fadar shugaban kasa saboda zarginsa da handame miliyoyin cfa.

Yaki da cin hanci da rashawa na kan gaba a jerin alkawuran da Mohamed Bazoum ya dauka a yayin da yake yakin neman zabe a watan Disamban 2020.

Haka kuma ya nanata wannan aniya a jawabinsa na rantsuwar kama aiki a ranar 2 ga watan Afrilun da ya gabata bayan bayyana shi a matsayin sabon zababben shugaban kasa.

Hakan ya sa shugaban ya kaddamar da shirin Operation ‘Ba sani Ba sabo’ domin tsaftace harkoki a ma’aikatun gwamnati, inda cin hanci da handama suka yi katutu matakin da shugaban reshen kungiyar Transparency International Maman Wada yace suna goyon bayansa.

A yanzu haka daya daga cikin daraktocin gudanar da al’amura a fadar shugaban kasa Ibrahim Amadou Moussa, ya bakuncin gidan yarin Say a ci gaba da binciken da binciken da ake kan badakalar daruruwan miliyon cfa, da ake zargin anciro ta bayan fage daga asusun baitul malin kasa da sunan fadar shugaban kasa a shekarar 2020.

Wannan almundahana na daga cikin jerin aiyukan asha da hukumar HALCIA ta ce ta gano a can baya sai dai daukan matakan hukunci ya faskara dalili kenan Malan Maman Wada ke cewa lokaci ya yi da za a kakkabe kurar dukkan wasu takardun zargin wawurar dukiyar kasa.

A washegarin shigarsa ofis, Bazoum Mohamed ya gana da shugabanin hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA, abin da ya basu damar gabatar da koke a game da tsaikon da ake fuskanta wajen isar da rahotanin hukumar zuwa mashara’anta mafari kenan shugaban kasa ya umurci ministan shari’a ya dauki matakin warware wannan kulli a karksahin shirin Operation Ba-sani Ba-sabo.

A jawabinsa na karbar ragamar shugabancin kasa Mohamed Bazoum ya lashi takobin hukunta mahandama dukiyar jama’a sannan ya kudiri aniyar yaki da cin hanci ba sani bas abo. Ya na mai cewa fakewa da kowane irin dalili ba za su kubutar da wadanda aka kama da aikata irin wannan laifi ba.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG