Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baya Ga Cutar Sankara, Sigari Na Haddasa Bugun Zuciya Da Shanyewar Bangaren Jiki


Wani mai shan tabar sigari
Wani mai shan tabar sigari

Wani rohoton Hukumar Lafiya ta Duniya ya gano cewa, yawan shan tabar sigari ya ragu sosai tun shekarar 2000 amma ba na yadda ake bukata ba domin cimma manufar da aka shata na rage yawan mace-mace daga cututtukan zuciya da sauran wasu cututtuka da shan tabar sigari ke jawowa.

A ranar da aka ware domin hankalin jama'a kan illolin shan tabar sigari ta wannan shekarar, Hukumar Lafiya ta Duniya ta hada hannu da Hadakar kungiyoyin yaki da cututtuka masu adabar zuciya ko WHF domin wayar da kan jama'a game da yadda shan taba ke haddasa cututtukan zuciya da ke hallaka kimanin mutane miliyan 17.9 a duk shekara.

Shan taba da kuma shakar hayakin tabar ga wadanda ba su sha, sune ke kan gaba wajen haddasa cututtukan zuciya da suka hada da bugun zuciya wato zuciya ta daina bugawa, da shanyewar bangaren jiki wato stroke, wadanda ke hallaka kimanin mutane miliyan 3 duk shekara.

"Yawanci ana sane da cewa shan taba na haddasa cutar sankara ko cancer a turance amma da dama ba su san cewa ta na haddasa ciwon bugun zuciya da shanyewar bangaren jiki ko stroke ba," inji Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus

Shugaban sashen yaki da cututtukan zuciya na hukumar lafiya, Dakta Douglas Bettcher, ya ce gwamnatocin kasashe na da karfin ikon kare jama'arsu daga kamuwa da wadannan cuttukan.

"Ta hanyar samar da matakan da za su taimaka wajen rage barazanar cututtukan zuciya kamar haramta shan taba a duk wuraren da ba a waje ba ne ba da kuma saka gargadi kan kwalayen tabar sigari da ke nuni da hadurran da ke tattare da shan tabar," inji Dakta Bettcher

A kowace shekara, shan tabar sigari na hallaka sama da mutane miliyan 7 duk da cewa ana samun raguwar shan tabar kamar yadda sabon rohoton hukumar lafiya 'Global Report on Trends in Prevalence of Tobacco Smoking 2000-2025' ya nuna.

Rohoton ya nuna cewa an samu raguwa, inda a shekarar 2000 kashi 27 cikin dari na jama'ar duniya ne ke shan taba amma a 2016, kashi 20 cikin 100 aka samu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG