Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, sun gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari da bakonsa, sun tattauna ne kan batutuwa da suka shafi tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma abin da ya shafi zabe.
Har ila yau sun tattauna kan batutuwa da suka shafi yadda Najeriya da Amurka za su bunkasa fannin cinikayya a tsakaninsu.
Yayin da yake yi wa manema labarai bayani, Tillerson ya yaba da irin rawar da Najeriya ke takawa a yakin da ake yi da 'yan ta'adda a yankin Tafkin Chadi, a cewar wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa.
Tillerson ya kuma kara jaddada muhimmancin hadin kai wajen yaki da 'yan ta'adda musamman masu alaka da kungiyoyi irinsu ISIS.
Sannan ya yaba da yadda Najeriya ta yi zabe cikin lumana a shekarar 2015 tare da nuna muhimmancin ganin irin hakan a badi.
Tillerson yana rangadin kasashe biyar ne da ke nahiyar Afirka da suka hada da Ethiopia da Kenya da Djibouti da Chadi da kuma Najeriya.
A yau zai kuma kama hanyarsa ta komawa Amurka, bayan da aka takaita tsawon ziyarar ta sa saboda bukatar ya koma ya fuskanci wasu batutuwa da suka taso, musamman kan batun Korea ta Arewa.
Wannan ita ce ziyarar farko da sakataren harkokin wajen Amurka karkashin gwamnatin shugaba Trump ya kawo nahiyar Afirka.
Saurari rahoton Umar Faruk Musa domin jin karin bayani:
Facebook Forum