Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya koma bakin aiki a ziyarar da yake yi a Kenya, bayan da ya soke halartar tarukan da aka tsara zai je a jiya Asabar, sanadiyar rashin lafiya da ya yi fama da ita.
A yau Lahadi, Tillerson ya ajiye kunshin furanni a ofishin jakadancin Amurka da ke Birnin Nairobi, a wani biki da aka yi domin karrama wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka mutu a harin bam din da aka kai wa ofishin shekaru 20 da suka gabata.
Bayan da ya gana da shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta a ranar Juma’a a Birnin na Nairobi, Tillerson ya yaba shirin sasanta rikicin siyasar kasar da shugaba Kenyatta da abokin hamayyarsa Raila Odinga suka fara.
Ya kuma kwatanta shirin a matsayin “gagarumin ci gaba da aka samu a fannin sasanta rikicin kabilanci da na siyasa da ya haifar da rarrabuwar kawuna,” kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta sanarwa.
Facebook Forum