Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tillerson Ya Kamu Da Rashin Lafiya


Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson
Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson

Rahotannin na cewa Sakataren harkokin wajen Amurka da ke rangadin wasu kasashe a nahiyar Afirka yana fama da rashin lafiya, yayin da ya isa Kenya a jiya Juma'a.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, yana hutawa, bayan rashin lafiya da yake fama da ita, yayin da yake ziyarar wasu kasashe a nahiyar Afirka.

Hakan ya sa, Tillseron ya soke zuwa wasu taruka da zai halarta a Kenya a yau Asabar.

A jiya Juma’a Sakataren na Amurka ya isa Kenya, a wani rangadin kasashe biyar da yake yi a nahiyar, wadanda suka hada da Ethiopia, Chadi, Najeriya da kuma Djibouti.

“Sakataren ba ya jin dadi, bayan ‘yan kwanakin da ya kwashe yana aiki kan wasu muhimman batutuwa a can gida, kamar batun Korea ta Arewa, saboda haka ya fasa zuwa turakan da zai je a yau.” Inji Kakakinsa, Steve Goldstein, wanda suke rangadin tare.

Goldstein ya kara da cewa, za a ci gaba da wasu taruka ba tare da shi ba, ana kuma sa ran gobe Lahadi zai murmure ya komo bakin aiki.

Bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Uhuru Kenyatta a jiya Juma’ar, Tillerson, ya ce yunkurin sasanta rikicin siyasar kasar Kenya, tsakanin Shugaba Uhuru Kenyatta da kuma shugaban ‘yan adawa Raila Odinga, na samun gagarumin ci gaba.

Yana mai cewa Amurka na goyon bayan duk wani mataki da zai sa a yi tafiya da kowa da kowa da kuma tabbatar da mulkin Dimokradiyya.

A karon farko, Kenyatta da Odinga sun hadu, tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi mai cike da rudani, a wani mataki na ganin an samar da tsaunin da zai kawo hadin kasa.

Tillerson ya yaba da wannan mataki da bangarorin biyu suka dauka a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi da ministar harkokin wajen kasar ta Kenya, Monica Juma, a Birnin Nairobi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG