Malaman sun karade wasu manyan titunan babban birnin jihar dauke da kwalaye cike da rubutu. Sun tafi hedkwatar hukumar dake kula da makarantun gaba da firamare kafin su zarce zuwa gidan gwamnatin jihar domin mika kokensu ga gwamnan jihar Murtala Nyako.
Malaman da aka daukesu aiki an turasu ne wasu garuruwa domin koyaswa. Masu zanga-zangar sun ce wata ashirin da biyu ke nan ba'a biyasu albashi ba. Kullum alkawari ake yi masu za'a biya yau ko gobe. Malaman sun ce sun shiga wani halin da sai dai Allah ne zai iya fitar da su. Sun ce yanzu kura ta kai bango. Sun kira shugaban kwadagon jihar cewa idan har ba za'a biyasu ba to duk makarantun jihar su tafi yajin aiki.
Amma duk kokarin da malaman suka yi domin su gana da gwamnan abun ya cutura. Saidai wasu hadiman gwamnan sun fito sun kira wasu shugabannin malaman sun shiga wani zaure da su. Wannan zanga-zangar ita ce ta bakwai tun lokacin da aka daukesu aiki lamarin da yasa majalisar jihar ta sa baki.
Kungiyar kwadago ta sha kokawa akan lamarin da yin fafitikar ganin an biya malaman. Dauda Maina shugaban kwadagon jihar kuma shugaban kungiyar malamai ta NUT yace a kungiyance suna tare da malaman dari bisa dari. Yace babu yadda za'a dauki mutum aiki ba'a biyashi ba har fiye da shekara daya. Idan da wani wurin ne da an yi kone-kone.
Zanga-zangar malaman na zuwa ne yayin da majalisar dokokin jihar ta ba gwamnan 'yan kwanaki ya biya ma'aikatan jihar albashin watanni biyu da bai biya ba kana gwamnatin ta mayar da wasu kudade da aka zaftare daga albashin ma'aikata ko kuma su dauki mataki akan gwamnan.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.