Wani da ya zanta da wakilin Muryar Amurka a jihar Adamawa yace akwai abubuwa dake faruwa da suke tayar masu da hankali. Da zara sun shiga gidajensu da wuri wasu bata gari suna fasa masu shaguna da shiga wasu gidaje su yi gaba da dukiyoyi. Dokar hana fita ta hanasu fita amma bata hana bata gari fita ba domin dokar bata aiki akansu. Wasu miyagu na iya fita har su je su yiwa mutane barna a shaguna da gidaje.
Dangane da abubuwan da yakamata a yi domin dokar ta baci ta samu nasara, mai fira da wakilinmu yace ita dokar tana da bangarori guda hudu kuma dole a kiyayesu kafin ta samu nasara. Tun da aka kafa dokar bangare daya a keyi cikin hudun. Bangaren farko shi ne bangaren mulki. Shugabanni yakamata su dauki matakin ba sani ba sabo. Wadanda ake cewa basa biyan jami'an tsaro alawus nasu a bincika idan an samesu da laifi a hukumtasu.
Bangare na biyu shi ne difulomasiya. A nemi hadin kan kasashen dake makwaftaka da Najeriya da hadin kan mazauna jihohin dake cikin dokar ta baci da hadin kan shgabannin siyasa da na addini. Misali an sake sabunta dokar amma ba'a tuntubi shugabannin siyasa ko na addini ba ko sarakuna. Idan babu tuntubar juna ba za'a yi nasara ba.
Abu na uku shi ne batun tattalin arziki. Dokar ta durkusar da tattalin arzikin jihohin dake ciki. A jihar Borno kawai an lalata makarantu sama da dari takwas kana ga masu gudun hijira da aka rabasu da gidajensu da ayyukansu. Dole a ce akwai tallafi. Amma cikin shekara guda babu wani tallafi.
Sojoji kuma su yi aikinsu da tausayi ba tare da tsawalawa mutane ba. Abu na karshe a nemi goyon bayan wadanda aka kaka masu dokar ta baci.
Ga rahoto.