Jaridar ”The Leadership” ce ta bada rahotannin dake cewa an sami hafsoshin sojojin Najeriya da laifin samar da muhimman bayanan tsaro da kuma wuraren da rumbunan makaman sojojin Najeriya suke ga mayakan “Boko Haram”.
Kungiyar da ake yawaita zargin da hannu wajen kisan mutane masu tarin yawa acikin shekaru biyar da suka gabata a Najeriya.
Amma kuma yau laraba manyan jami’an Najeriya da suka hada da kakakin rundunar sojojin Najeriya Manjo janar Chris Olukolade da kuma babban jami’an ayyukan sadarwa r Gwamnati Mike Omeri,dukkansu biyun sun shaidawa muryar Amurka cewa babu kanshin gaskiya a rahotannin da aka bayar.
Wani babban abin damuwa shine da har yanzu ana zargin Boko Haram da ci gaba da rike ‘yan matan makarantar nan sama da dari biyuda suka sace daga wata makarantar sakandare a jihar Borno,a Najeriya tun watan Afrilu da ya gabata.