Wasu tsoffin 'yan jam'iyyar PDP kamar Yarima Muri Isa Tafida dan kwamitin zartaswar jam'iyyar gani suke matsayin uwar jam'iyyar bai dace ba domin hakan ka iya yiwa jam'iyyar da dimokradiya illa. Ya ce babu matsalar da za ace ba za'a iya sasantawa ba. Masu nuna halin ko a sasanta ko kada a sasanta basu damu ba rashin hankali ne. Duk wani mai hikima zai nemi sasantawa. Wanda ba ya son hakan bashi da hankali. Ya ce shi kuma ya san su manyan PDP suna da hankali. Ya ce damuwa ce ace gwamnoni bakwai sun koma sun zama 'yan adawa. Ya ce amma su dattawan jam'iyyar ba zasu bari su fita ba domin tun shekarar 1999 mutane sun karbi jam'iyyar sai kuma a karshen 2013 su barta. Ya ce idan sun yi hakan mutane suka yaudara. Don haka dole su sake zama su shirya.
Tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da APC ta nemi gafara wurinsa domin kokarin shigowa da gwamnonin 'yan tawayen PDP ba tare da tuntubarsa ba ya ce ya yi maraba da su. Ya ce duk wani dan siyasa yana son kari ko na mutum daya ne domin bai san abun da mutum dayan zai yi masa ba. Shigowarsu karuwa ce ta karfafa jam'iyyar APC. To amma ya yiwa jam'iyyarsa kashedi. Ya kada shugabannin su sake a kokarin neman gira a zo a rasa ido. Ya ce idan ba an bi sharudan da shi da can ya bayar ba to za'a yi kitso ne da kwarkwata.Yana nufin a daidaita yadda babu wanda zai rena wani a kan kowane dalili domin a tafi lafiya.
Sai dai wasu na ganin kin shigar Sule Lamido da Babangida Aliyu jam'iyyar APC suna gudun cinikin biri ne a sama domin jam'iyya adawa bata bata kafa gwamnati ba a Najeriya.
Ga karin bayani.