An kashe mutane akalla 20 yau laraba a yankin arewacin Kamaru, a wasu hare-haren kunar-bakin-waken da jami'ai suke dora laifin kai su a kan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram daga makwabciyarsu Najeriya.
Hare-haren sun wakana lokaci guda a wata kasuwa da kuma wata unguwa dake Maroua, babban birnin Jihar Arewa mai Nisa ta Kamaru.
Wani dan kasuwa dake wannan kasuwa ta birnin Maroua, Ousmaila Toukour, ya shaidawa VOA cewa daruruwan mutane sun ji rauni, kuma an garzaya da su asibiti.
Gwamnan Jihar, Midjiyawa Bakari, yace hukumomi su na gudanar da bincike, amma kuma yace yana karfafa zaton wannan aikin ta'addancin na kungiyar Boko Haram ce.
A makon da ya shige Kamaru ta haramta sanya Niqab a bayan da maharan Boko Haram suka tayar da bama-bamai a garin Fitokol dake kan iyakar kamaru da Najeriya. Maharan mata ne da suka rufe fuskokinsu da Niqab.