Bakin haure fiye da 900 daga kasashen Afirka jiragen yakin ruwa na wasu kasashen turai suka cetosu daga tekun Bahar Rum.
Bayan sun yi wasu kwanaki da aka cetosu an kaisu kudancin kasar Italia jiya Talata.
Jirgin kasar Norway Siem Pilot ya kawo bakin haure kusan 240 yawancinsu daga Eritrea. Ya kaisu tashar jirgi dake Mesina a Sicily da safiyar jiya.
Kazalika da rana jiya din jirgin Birtaniya Enterprises shi ma ya kai bakin haure fiye da 650 su ma yawancinsu 'yan asalin Eritrea ne. Jirgin ya kaisu Catania a Sicily.
Jami'an tarayyar kasashen turai sun shaidawa Muryar Amurka cewa an ceto bakin hauren ne biyo bayan kiran gaggawa da jami'an Italia suka samu jim kadan bayan da jirgin dake dauke dasu ya bar gabar tekun Libya.
Mafi yawan fasinjojin maza ne amma akwai mata da yara cikinsu.
Kungiyar bada agaji ta Red Cross da kungiyar kare yara ko Save the Children da wasu kungiyoyin duk sun kasance a tashoshin jiragen ruwan Sicily domin su bada taimako. Sun duba lafiyar bakin hauren kafin su yi masu rajista tare da sasu cikin motocin safa safa.
Wani wakilin Muryar Amurka da ya samu damar shiga cikin jirgin Norway yace bakin hauren suna cikin gajiya amma sun yi murna sun isa kasar turai lafiya.
Bakin hauren suna cikin mutanen da suka fuskanci matsaloli a kasashensu walau a Afirka ko Gabas ta Tsakiya. Dole ta sa suka dukufa ga tafiya mai hadarin gaske, wato ketare tekun Bahar Rum zuwa kasar turai.
Hukumar dake kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ambato makon jiya cewa za'a samu bakin haure fiye da 700,000 da zasu nufi nahiyar turai daga hanyar tekun Bahar Rum kafin karshen wanan shekarar.
A wata sabuwa kuma ana kyautata zato kungiyar tarayyar turai zata soma rarraba bakin hauren daga kasashen da suka yi yawa kamar su Italia da Girka zuwa wasu kasashen cikin wannan makon.
Yayin da yake jawabi a Zagreb babban birnin Croatia kwamishanan bakin haure na tarayyar turai Dimitris Avramopoulos ya fada jiya Talata cewa rukunin farko da ya kunshi 'yan Eritrea za'a turasu zuwa kasar Sweden ranar Juma'a.
Rukunin na cikin mutanen farko su kusan 40,000 da kungiyar Turai zata rarraba nan da shekaru biyu.