Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tekun Baharum Ya Cinye Bakin Haure Arba'in


Bakin haure da aka ceto daga tekun baharum
Bakin haure da aka ceto daga tekun baharum

Kungiyar dake kaiwa yara dokin gaggawa tace an ceto 'yan cirani ko bakin haure da dama daga tekun baharum amma wasu guda arba'in basu ci sa'a ba.

Kungiyar kai dokin gaggawa ga yara ta "Save The Children" tace da alamar ruwa ya ci wasu bakin haure ko 'yan cirani kimanin 40 a ranar Lahadi a Tekun Bahar Rum, bayan da kwalekwalensu na roba da ake kunbura shi da iska, au ya sace au ya yi bindiga, yayin da su ke kokarin zuwa gabar tekun Italiy

Kungiyar ta jinkai, ta ce wadanda su ka rayu sun fadi cewa mutane da yawa sun mutu, bayan da su ka fada cikin tekun kuma su ka kasa iyo. Su ne na baya bayan nan bayan da mutane kimanin 1,750 da su ka mutu, a cigaba da kwararan 'yan gudun hijira babu kakkautawa, wadanda ke kokarin guje ma tashe-tashen hankula da fatara a Afirka da kasashen gabas ta tsakiya.

An samu wannan rahoton mace-macen ne daga wasu 'yan Ghana da Gambia da Senegal da kuma Ivory Coast, wadanda su ka samu tsira da rayukansu, bayan da su ka isa tashar jirgin ruwa ta Catania da ke kasar Italiya.

Jiragen ruwan sojojin Italiya da na dogarawan tsaron gabobin ruwa, sun ceto wasu 'yan ci-rani wajen 6,800 a karshen makon jiya; sannan kuma jirgin ruwan sojin Italiya mai suna Bettica ya isa da wasu 'yan ci-ranin wajen 652 Italiya jiya Talata.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG