Kyaftin Nick Cooke-Priest, ya ce akwai bayanai da ke nuna cewa wasu bakin haure dubu 450 zuwa dubu 500 daga Libya, suna jira a bakin teku domin a kwashe su zuwa nahiyar ta turai.
A yau Lahadi, ma’aikatar tsaron Burtaniya ta ce an aika da wani jirgin ruwan kasar mai suna Bulwark, domin ya ceci wasu bakin haure 500, bayan da wani jirgi mai saukar ungulu ya hangi kwalakwalensu guda hudu.
Har ila yau wani jirgin ruwan Italiya da ya kwaso wasu mutane 316 da suka taso daga Libya, ya isa gabar tekun yankin Lampedusa.
A ‘yan watannin nan, an samu kwararar bakin haure da dama zuwa nahiyar turai, lamarin da masu fashin baki ke cewa na da nasaba da rashin doka da oda a Libya, wanda hakan ke bude kofar kwararar bakin hauren ta kasar.