Masu tsaron gabar Tekun kasar Italiya, sun ceto wasu bakin haure fiye da 4,200 a yankin Meditareniya.
Jami’an sun samu taimakon sojin ruwan kasar da na Jamus da kuma kasar Ireland, wadanda kasashe ne daga nahiyar Turai da suke gudanar da aikin hadin gwiwa daga Nahiyar Turai.
Sun kuma ce sun gano gawawwakin mutane goma sha bakwai, amma babu bayanai kan me ya haddasa mutuwarsu.
Sai dai jami’an Italiya na danganta irin wannan mutuwa da matsanancin halin gajiya da kishin ruwa da bakin hauren kaiya shiga, yayin da suke kokarin shiga nahiyar turai.
A ‘yan kwanakin nan an samu kwararar bakin hauren da dama, kuma masu sa ido a lamarin sun ce rashin doka da oda da kasar Libya ke fuskanta da matsanancin halin da yankin Afrika ta Arewa ke fuskanta, na daga cikin ababan da ke haddasa yin kaura.