Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bada Jimawaba PDP Zata Dawo Idan APC Bata Shirya Gidan ta ba


Majalisar Najeriya
Majalisar Najeriya

Jamiyyar PDP, na kokarin ci gaba da bada hakuri, ga wadanda suka samu matsala a cikin ta saboda wacen dalilin yanzu babu shi, kuma mutane suna sha’awar jamiyyar don wadanda ake maganan cewa ana zawarcisu dama ‘ya’yan PDP, ne suka yi fushi saboda wani dalili to wannan dalilin ya kau.

Mataimakin kakakin jamiyyar PDP, Barrister Abdullahi Jalo, ne ya bayana haka ga wakilin muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, yana mai cewa wadanda suka kaura daga PDP, da suke majalisar Dattawa da kuma manya-manyan jiga-jigai na kasa duk suna nan da zuciyar PDP.

Koda yake a kwanakin nan sai da shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya fadi cewar shi da APC, kam yazo Kenan.

Dangane da haka sai Barrister Jalo, yace “ Baza ace komai ba tunda shi shugaban majalisar Dattawa ne kuma Jamiyyar APC, yake wakilta, Bukola Saraki bai taba yin wata jamiyya ba Tambuwal ma da yake PDP, an ace masa yana APC, bai taba cewa zai bar PDP, ba yanzu ba yana Gwamna a APC, ba zuciyarsa ya canja ne daga ra’ayi da akidar PDP.”

Barrister Solomon Dalung, na jamiyyar APC, yace “ PDP, bata da wasu ‘ya’ya na kwarai dama ‘ya’yan wasu ta gada idan ka gaji dan wani to ka sani cewa yana da gidan ubansa, saboda haka wadannan ‘yan adawa ne sun kuma ci zabe a karkashin adawa kuma ba zasu je koina ba.”

Buhari Bello Jega, wani Malamin kimiyar siyasa a jami’ar Abuja, cewa yayi idan jamiyyar APC, bata iya shirya gidan ta ba lalle bada jimawaba zamu ga dawowar PDP, da karfinta saboda har yanzu suna rike da kasar kuma suna da mulki suna da kudi suna da mutane suna da Gwamnoni goma sha hudu, saboda haka ba za’a iya cewa PDP, ta mutu gabadaya ba to amma tana kokarin mutuwa ne, idan har jamiyyar APC, bata yi kokarin nuna cewa abun da ya faru a majalisa ba daidai bane kuma zata hukumta wadannan mutane to tana iya tuzurasu har su bar jamiyyar.

XS
SM
MD
LG