Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsabta Cikon Addini, Matasa A Kula


Tsabtar muhalli muhimmin abu ne a al'umma. Ko wacce irin rawa ya kamata matasa su taka wajen tsabtace muhallansu?

Dandalin VOA ya gana da Ummar Saleh Ankah, mataimakin Shugaban kungiyar masu kula da muhalli ta kasa. Malam Ummar yace akwai sauran runa a kaba a fannin yadda ake kula da muhalli, ba za 'a ce gwamnati bata yi kokari ba wajen kula da muhalli.

Ya cigaba da cewa, daga gwamnatin Tarraya Zuwa jiha ( kamar jihar Kano inda yake zaune), an yi kokari bakin gwalgwado wajen gyara hanyoyin kwatoci abinda shine babbar matsalar da ake fuskanta a cikin birane.

Amma abinda ya rage shine gwamnati ta dage wajen hukunta masu laifi, ya kamata ace Hulda ta muhalli itama a sa mata wata doka da kuma wata chibiya da zata dinga sa ido a Kai, a cewar malam Ummar.

Akwai abubuwan da ya kamata a ba muhimmanci kamar sharar karshen wata, a da an fi ba dokar muhimmanci sosai amma yanzu matsalar da ake samu ita ce, ko a gida ma ba sharar ake ba. Don haka ya kamata a canza tunanin mutane ta karfi da yaji don su san muhimmancin yin sharar.

Malam Ummar ya kuma ce, duk da cewa Ana yin sharar a karshen kowane wata, amma ba yadda ya kamata ba. Ga Baraka Bashir da rahoton.

XS
SM
MD
LG