ABUJA, NIGERIA - Hafsan Hafsoshin ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin wani babban taro na manyan kwamandojin rundunar mayakan Najeriya, domin duba yanayin tsaro a kasar,
Janar Yahaya wanda ya ce IPOB da ESN a baya sun yi barazanar hana gudanar da zabe, ya jaddada cewa, da zabe ko ba zabe babu wata kungiya ko kungiyoyi, koma gungun wasu mutane da za a bari suyi wa Najeriya barazana, kasancewarta kasa daya dunkulalliya.
A cewarsa, biyo bayan irin matakan ba sani ba sabo da sojojin da sauran jami'an tsaro ke dauka yanzu Najeriya na hako gangar mai miliyan daya da dubu dari uku a kullum kamar dai yadda kungiyar kasashe masu arzikin mai ta duniya ta tabbatar.
Babban hafsan mayakan Najeriyar wanda ya ce irin wannan taro da suka yi a Sakkwato a shekarar da ta gabata, matakan da aka dauka sun yi tasiri wajen samun gagarumar nasarar da mayakan keyi a halin yanzu, ya kara da cewa, yanzu an hana yan ta'addan Boko Haram sakat.
A hirar shi da Muryar Amurka, masanin tsaro Air Commodore Baba Gamawa ya ce dakarun kasar sun cimma gagarumar nasara ba ma kawai a Arewa maso Gabas ba, amma har da sauran sassan kasar.
To sai dai a nashi bayanin, shugaban kungiyar rundunar adalci a jihar Sakkwato Basharu Altine Guyawa Isa ya ce ba wata nasara da za ace an cimma tunda har yanzu ‘yan bindiga dadi na kara mike kafa tare da cin zarafin mutanen yankin Arewa maso Yammacin kasar
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina: