Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Zai Sanya Takunkumin Hukunta ‘Yan Damfara Ta Kasuwar Canji - Gwamnan CBN


Banban Bankin Najeriya CBN
Banban Bankin Najeriya CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, a ranar Juma'a yace za a ladabtar da hukumomin da ke da hannu wajen yin damfara a kasuwar canji, bayan wani bincike da aka gudanar ya taimaka wajen dakile ta'addancin da ake yi na biyan kudade "ta daidaituwar lissafi."

WASHINGTON, D.C. - Wani bincike da aka gudanar na dala biliyan 7 na kudaden a bankin da ya ki ci ya ki cinyewa, an gano wasu kura-kurai da suka shafi cinikin dala biliyan 2.4.

Abubuwan da ba su dace ba sun hada da bacewar takardu zuwa wasu da ba su wanzu ba da kuma masu cin gajiyar karbar kudaden musaya na waje ba tare da izini ba.

"Ana tambayoyi game da wadanda ke cikin rukunin da aka keta, wanda muke duba sosai. Wadanda ke da alhakin za a hukunta su," in ji Cardoso a ranar Juma'a a wani zaman majalisar.

Kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Afirka na fuskantar gurguncewar karancin dala wanda ya sa kudinta ya yi kasa a gwiwa a 'yan makonnin nan, ko da yake Cardoso ya fada a ranar Talata cewa kudin dala ya fara samun inganci.

Shi ma a wurin zaman, mataimakin gwamnan babban bankin kasa Muhammad Sani Abdullahi, ya kara da cewa bankin na hada hannu da jami’an tsaro domin ci gaba da daukar mataki kan masu laifin.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG