Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Bada Umurnin Mayar Da Hedikwatar FAAN Legas


Filin tashin jirage na Murtala Muhammad da ke Legas (Facebook/FAAN)
Filin tashin jirage na Murtala Muhammad da ke Legas (Facebook/FAAN)

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin mayar da hedikwatar hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa FAAN daga babban birnin tarayyar kasar Abuja zuwa Legas.

WASHINGTON, D. C. - Hakan na dauke ne a cikin wata takarda da aka rubuta ranar 15 ga watan Janairu da aka mika wa Manajan Daraktan Hukumar ta FAAN, Olubumi Kuku, wadda ke cewa: “Ministan Sufurin Jiragen sama da ci gaban jiragen sama ya bayar da umarnin a mayar da hedikwatar Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) daga Abuja zuwa Legas. Ana bukata ka bayyanawa masu gudanarwa sakamakon da zai biyo bayan daukar wannan mataki na kaurar. "

A baya dai gwamnatin tarayya ta sanar da mayar da wasu muhimman sassan babban bankin Najeriya (CBN) da ke Abuja zuwa reshensa da ke Legas.

Da yake sanar da komawar, babban bankin ya ce: “Tsarin aikin ya mayar da hankali ne kan kyakkyawan amfani da harabar bankin. Da wannan tsari, za a kwashe ma’aikata 1,533 zuwa wasu cibiyoyin CBN da ke Abuja, Legas, da sauran rassa da basu da isassun ma’aikata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG