Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za A Yi Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Bauchi Ba – Gwamnatin Jihar


Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed

Gwamnatin Jihar Bauchi tace baza a gudanar da zanga-zangar gama gari na kasa ba domin bayyana halin kuncin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya, ta kuma bukaci wadanda ke son shiga su je wani wuri.

Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Barrister Kashim Ibrahim ne ya shaida wa manema labarai hakan yayin wani taro a fadar gwamnatin jihar Bauchin, inda yace a jihar Bauchi ba za a yi zanga zangar ba kuma wanda yake son shiga sai yaje wani wuri. An san Bauchi da zaman lafiya, wannaan shine matsayar Gwamnati”.

Sai dai Kungiyar Civil Liberty Organization jagorar zanga zangar ta ce babu gudu babu jada baya, zanga zangar zai gudana kamar yadda aka shirya.

A nasa bayanin game da shirin zanga zangar, Shugaban Kungiyar Civil Liberty Organization shiyyar Arewa Maso Gabas,Comrade Muhammed Aliyu Wayas, yace sun shirya tsab don fara gudanar da zanga zanga daga ranar 29 ga watan Yuni da muke ciki.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG