Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Wani Matashi Yin Tattaki Daga Nijar Zuwa Najeriya


Wani matashi dan kimanin shekara 32, mai suna Jamilu Abdullahi ya soma tattaki daga birnin Niamey na Jamhuriyar Nijer zuwa Babban Birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Manufar matashin ita ce don ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, da ya cika shekaru 74 a duniya.

Wakilin Muryar Amurka ya yi kicibis da matashin a lokacin da ya biyo ta jihar Sokoto akan hanyarsa ta Abuja.

Jamilu Abdullahi wanda dan asalin garin Gusau ne a jihar Zamfara, yana zaune a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijer, inda daga can ne ya fara tattakin.

Matashin ya isa jihar Sokoto domin ya ga tsohon gwamnan jihar Attahiru Dalhatu Bafarawa ya gaya masa wannan aikin da ya dorawa kan sa, amma bai yi sa'ar ganin shi ba.

Ko gwanin nasa wanda yake wannan tattakin domin taya sa murna ya na sane da wannan jan aikin da da ya sa a gaba?

Matashin ya ce, tsohon mataimakin shugaban Najeriya bai san da shi ba, kawai dai soyayyace da kauna da yake yi masa.

Ranar 10 ga wannan watan Nuwamba ne ya ta so daga Niamey, ya yi kwana 7 a hanya kafin isowar sa jihar Sokoto.

Matashin dai ya yi fatan samun kwarin guiwa da jarumtaka domin ganin cewa hakar sa ta cimma ruwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG