Fulani dubu biyu da dari bakwai da saba’in da takwas ne za su amfana da wannan shirin, wanda za a rika bin su ruga-ruga ana taimaka musu da abin yin sana'o'in da za su hana su zaman banza wanda kan iya jefa su ga aikata munanan ayyuka.
Mai dakin gwamnan jihar Kebbi, Aisha Abubakar Atiku Bagudu, ita ce ta kaddamar da shirin tare da bayyana cewa an fito da shi ne bisa la'akari da irin fitintinnu da ke faruwa a Najeriya, inda akasari ake nuna yatsa akan Fulani.
A karkashin wannan shiri dai an rarraba kananan dabbobi da suka hada da Tumaki da Awaki da Kaji ga Fulani, domin su rika kiyo suna sayarwa domin samun abin lalura.
Aminu Garba Dan Diga, shine kwamishinan kula da lafiyar dabbobi a jihar Kebbi ya ce an karkasa shirin ta yadda dukkan Fulani dake jihar za su amfana.
A can baya ma, gwamnatin Najeriya ta fito da shirin Ruga inda aka yi niyar tsugunar da Fulani makiyaya wuri daya, a samar musu dukkan abin da suke bukata wajen gudanar da rayuwar su maimakon yawace- yawacen kiwo, sai dai shirin ya hadu da suka musamman daga jihohin Kudancin Najeriya.
Sai dai ko bayan dakatar da shirin a matakin tarayya, gwamnatin jihar Zamfara ta dukufa ga ganin ta gudanar da wannan shirin, inda aikin ginin wurin da shirin zai gudana yana kan tafiya.
Masana halayyar Dan Adam, kamar Farfesa Tukur Muhammad Baba na ganin cewa irin wannan shirin kan iya yin tasiri ga magance ayyukan ta'addanci.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.