Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP, na kasa baki daya Barrister Abdullahi Jalo, ya bayyana cewa Gwamnonin Najeriya, baki daya na jamiyun PDP, da APC, sun gudanar da wani taron siri gabanin zaben shugabanin majalisu wakilai da na dattijai, inda suka tsarar da yadda aka zabo shuwagabanin majalisun biyu.
Ya kara da cewa duk Gwamnonin jamiyun biyu sun yi ittifaki cewa yadda aka yi shine zai sa kasar ta dinku,domin a wancen subi na Gwamnatin da ya shude abun ya zama bangare daya, inda an zama bangare daya kuma abun da ake harsashe kasar zata ruguje.
Ya furta haka ne a hira da wakilin muryar Amurka Hassan Maina Kaina, yana mai cewa Gwamnan Sokoto na APC, Aminu Tambuwal, ne ya fara yiwa Abubakar Bukola Saraki, murna yace ko kuma a cikin Gwamnonin wanene yace za shi kotu dagane da wannan zaben.
A bagare daya kuma APC, ta bakin Barriter Solomon Dalung, ta yi watsi da wanan ikirari na PDP, da cewa suna neman hada rigima ne a jamiyyar APC, domin idan APC, ta amince da wannan munafincin da suke so su shuka to sai jamiyya ta fara kai ruwa rana wanda hakan sai basu damar cin gajiya.