Da take magana Oluremi Tinubu uwargidan tsohon gwamnan Legas Sanata Ahmed Tinubu tace tun da gwamnati mai ci yanzu ta hau mulki babu abun da ake yi sai sunkunle da shirme. Tace ana batun cin hanci da rashawa da batun tabarbarewar tsaro da batun rashin aiki kana ba'a san inda gwamnatin ta sa gaba ba. Idan shugaba Jonathan ya san ba zai iya ba to gwamma ya sauka domin a samu wanda zai iya wannan aikin. Tace kasar nada wadataccen kudin da za'a iya kula da tsaro amma sai shirme a keyi.
Ita ma shugaban mata ta jam'yyar reshen Legas tace mai girma shugaban kasa muna ganin abubuwan dake faruwa suna nuna rashin kwarewa wajen hubbasan da ka keyi domin kare wannan kasar. Domin haka akwai bukatar ka kara kaimi domin inganta matakan tsaro a cikin kasar.
Da yake mayar da martani mataimakin kakakin jam'iyyar PDP Barrister Ibrahim Jalo cewa yayi menene ma'anar kasawa ne a Hausa. Yace kasawa ita ce ka soma abu ka kauce masa. Yace duk shekarun da PDP tayi tana aiki ta daina ne. Shin wai sai yanzu ake cewa ta kasa. A ina ne ta kasa.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.