Wata majiya daga cikin jam’iyyar ta shaida cewa shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin sun karkatar da akalar shugabanci jam’iyyar ga duban yan takara hudu da suka hada da tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura da Sanata Abdullahi Adamu; tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ta CPC da aka yi hadaka da ita a baya, wato Saliu Mustapha, sai kuma tsohon ministan ma’adinai da karafa, Abubakar Bawa Bwari domin zabar shugaban jam’iyyar na kasa.
Saidai sanata Abdullahi Adamu wanda shi ne shugaban kwamitin sulhu na jam’iyyar APC, da kuma Bawa Bwari wanda ya kasance minista a wa’adin mulkin shugaba Buhari karo na farko ba su nuna sha’awarsu a takarar ba a hukumance kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.
Majiyoyi daga fada shugaban kasa sun ce wani sashe na fadar shugaban na duba su a matsayin wadanda za su maye gurbin gwamnan jihar Yobe kuma shugaban riko na jam’iyyar, Mai Mala Buni.
Duk da cewa jam’iyyar APC ta yi watsi da rahoton da ya mamaye kafaffen yada labarai da ke cewa ta ware mukamai ga ’yan takara hudu da ake tunanin za su yi takarar kujerar jam’iyyar wadanda dukansu sun fito ne daga shiyyar Arewa ta tsakiya.
Kazalika, ana ci gaba da yada jita-jitar cewa alamu na nuni da cewa fadar shugaban kasar na goyon bayan tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura ya sami kujerar.
Duk da cewa wata majiya ta ce akwai matukar wahala a karanta tunanin shugaba Buhari kan wannan al’amari na wanda ya ke goyon baya don ya sami kujerar, sai dai ana tsammanin yanayin shugaban ya nuna cewa ya fi bada fifiko ga Al-Makura, wanda shi ne gwamna daya tilo da jam'iyyar CPC ta samar kafin aka yi hadaka aka zama APC.
Haka kuma, wasu bayanai sun tattaro cewa tuni magajin Al-Makura a jihar Nasarawa, gwamna Abdullahi Sule, ya fara tuntubar takwarorinsa gwamnoni da dama domin marawa magabacin nasa baya domin ya sami kujerar shugaban jam’iyyar ta kasa.
Saidai masu adawa da shi Al-Makura din sun jawo hankalin masu tallata shi don ya sami kujerar cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa na kan kan gudanar da bincike a kan sa.
Idan ana iya tunawa, Almakura da mai dakinsa Haj. Mairo Al-Makura sun ziyarci ofishin hukumar EFCC a ranar 29 ga watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2021.
An dade ana kai-kawo kan batun gudanar babban taron jam’iyyar APC Mai mulki wanda a cikin makon nan ne dai jam’iyyar ta tsaida ranar 26 Fa watan Febrairun Dan gudanar da shi.