Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Tana Jan Kunnen Matasa su Guji Fitina da Sunan Siyasa


Hoton Matasa da suke neman canji.
Hoton Matasa da suke neman canji.

Shugaban matasan APC Dasuki Jalo Waziri ne yayi kiran a wani taron fadakarda da aka shirya domin haka.

Da yake magana a wajen bude taron fadakarwan, shugaban matasa na babbar jam'iyyar hamayyar ta APC Ibrahim Dasuki Jalo, yace babu ci gaba da za'a samu in ba tareda zaman lafiya ba.

Daga nan ya sake nanata kiran da jam'iyyar take yiwa magoya bayanta cewa su tabbata sun "kada kuri'unsu kuma su tsare sannan su raka". Domin kamar yadda yadda yace, basu amince da su kada kuri'a su tafi gida su jira sakamako ba.

Ana sa bangare, wani tsofon soja, keftin Bala Jibrin, wanda ya ziyarci inda aka yi taron fadakarwan, yace yanzu lokaci yayi da magoya bayan jam'iyyar PDP zasu gane cewa, lokacin barinsu mulki yayi.

Amma Adamu Maina Waziri yace da yawa cikin 'yan jam'iyyar APC, mutane ne marasa gaskiya, wadanda suke fakewa da janar Buhari domin su boye irin barnar da suka yi.

APC Tana Jan Kunnen Matasa su Guji Fitina da Sunan Siyasa - 2'57"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG