Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a Najeriya, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya gudanar da gagarumin gangamin yakin neman zabe a Kano a yau talata.
An bayyana wannan taro na yau a zaman daya daga cikin mafiya girma na siyasa da aka taba gudanarwa a birnin, wanda kuma shi ne mafi girma a duk yankin arewacin Najeriya.
Janar Buhari ya fadawa magoya bayansa cewa babban abinda zai mayarda hankali a kai idan ya zama shugaban kasa, shi ne magance matsalar rashin tsaro, da rashin aikin yi da kuma yakar cin hanci da rashawa.
Manyan jam'iyyar APC da dama sun halarci wannan gangamin, cikinsu har da gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso wanda ya bayyana abinda ya gani a wurin taron a zaman alama ta cewa Kanawa dai sun zabi Buhari a zaman shugaban kasarsu.
Shi ma kakakin majalisar wakilan tarayya ta Najeriya, wanda yake takarar kujerar gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, yace jam'iyyar APC ita ce jam'iyyar da zata iya magance matsalolin dake fuskantar 'yan Najeriya.
Dukkan wadanda suka yi jawabai, tun daga kan shi Janar Buhari, sun roki jama'a da su tabbatar da cewa sun samu katunan zabensu, su kuma tabbatar da cewa sun jefa kuri'a sun tsaya an kirga da su a wurin.