Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben APC a Jihohin Bauchi da Gombe Ya Bar Baya da Kura


Zaben fitar da shugabannin anguwanni da APC ta gudanar a duk fadin kasar ya bar baya da kura a jihohin Bauchi da Gombe.

Zabukan fitar da shugabannin anguwanni a duk fadin Najeriya, sun samu matsala a jihohin Bauchi da Gombe.

A jihar Bauchi, an dage zaben har zuwa ranar Laraba, domin baiwa masu son shiga takara damar sayen takardar shiga takarar, kamar yadda jami'in da aka turo jihar Dr. Almajiri Geidam ya bayyana.

A jihar Gombe kuma, wasu 'yan takarar sunyi zargin cewa an hanasu sayen takardar shiga takara ma gaba daya. Wani Umar Ibrahim, yace "su ba zasu ce zabe ba ne amma nadi ne aka yi. Ba'a yi zabe ba. Nadi kawai aka yi aka ce masu an riga an gama zaben." Yace "a nasu wurin babu wanda ya zo ya gudanarda zabe amma an fitar da wanda suka ya ci." Ya kara da cewa ya je bankin ya biya kudi nashi da na sauran mutanensa. Yace "sun biya amma har washegari ba'a basu takardar tsayawa zabe ba."

To saidai wani mazaunin anguwar Yaro Gana, yace anyi zabe. Kwamared Garba "yace zabe ya gudana, kuma an yishi lafiya, kuma an gama lafiya a Yarwa Gana, inda na yi zaben." Yace batun cewa an hana wasu sayen takardar zabe, magana ce ta 'yan adawa da baragurbi.

Dangane da korafin mutane, shugaban riko na jam'iyyar APC a jihar Gombe Muhammed Dohu, yace ba gaskiya bane domin duk inda mutum yaci, an dauki hotonsa da bidiyonsa.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG