Daya daga cikin dabarun shi ne yadda 'yan siyasa ke manna hotunan wadanda suke so su yi masu takara a 2015. Wannan ya biyo bayan rangadin da shugaba Jonathan ke kaiwa wasu jihohin da ya hada da karbar wadanda suka sake canza sheka suka dawo PDP. 'Yan adawa sun ce rangadin ba komi ba ne illa kamfen din neman zaben 2015. Amma PDP tace ziyarar aiki shugaban ke yi.
Jauro Hammadu dan radun kare muradun PDP a arewa maso gabas yace idan an ce shugaban kasa to duk kasa tashi ce kuma a duk lokacin da ya ga dama zai je inda yake so. Yace shi bai dauki ziyarar da shugaban kasa ke yi a matsayin kamfen ba. Da aka tambayeshi ko yana goyon bayan shugaban kasa ya zarce da mulki sai yace shi ba zai bada amsa yanzu ba. Yace idan lokacin ya kai zai bada amsa. Zagaye zagayen da shugaban kasa ke yi na neman yadda kasar zata zauna lafiya ne.
Dantani D. O. shugaban kungiyar matasan arewa yana zagawa jihohi domin manna hotunan shugaba Jonathan. Yace sun fito su wayar da kawunan 'yanuwansu na cewa a bar siyasar addini ko ta kabilanci ko ta nuna wani abu can daban. Yace su bada goyon baya kana su fadi abubuwan da za'a yi masu.
Amma dan adawa Useini Gariko na ganin PDP na wuce gona da iri. Yace inda a ce wata jam'iyya ce take zagayawa tana kamfen ta bayan fagge da shugaban hukumar zaben ya taka mata birki.Amma da yake shugaban ne ke da hukumar sai abun da ya ga dama yake yi. Ai ma jam'iyyar APC yakamata tana zagayawa ta wayar da kawunan mutane domin sabuwar jam'iyya ce.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.