Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu 'Yan Arewa Na Sukar Taron Kasa


Duk da cewa taron kasa na cigba da gudana har yanzu wasu 'yan arewa suna sukar taron wanda suke kwatantawa da taron da na shan shayi kawai.

Duk da cewa tafiya tayi nisa a taron kasa, wasu 'yan Najeriya musamman 'yan arewa na cigaba da sukar lamirin taron, da suka ce bazai tsinanawa kasar komi ba.

Masanin harkokin siyasa kuma masani a harkar tsaro, Dr. Usman Bugaje yana ganin su kansu mahalarta taron basu san manufar taron ba. Yace "ba taron kasa ba ne amma taron shugaban kasa ne. Shugaban kasa ne ya zabosu ya kaisu suna shan shayi domin basu san dalilin taron ba. Su kansu mahalarta taron basu san dalilin taron ba." Yace rabin masu halartar taron ma barci su keyi.

Dr. Usman ya kara da cewa "babu wata matsalar kasar da taron zai warware sai dai ya kara dagula harkokin kasar. Daga yadda aka shirya taron kowa ya san ba zai haifi da mai ido ba." Yace yana tsoron kila an shuka wani abu ne, wanda su mahalarta taron ma basu sani ba.

Yace idan ana son a kawar da matsalar Najeriya, to a kawar da miyagun mutane dake kasar. Kowa yana ganin ana sa soja a hanya, ya hana zabe ko kuma dansanda ya dauki akwatin zabe ya ruga da shi. Yace ana canza alkamlumma na karya.

Shi ma Barrister Solomon Dalung na cikin wadanda ke ganin taron nada wani boyayyen manufa. Yace "taron kasa taron kwamiti ne, na neman zabe amma ba na kasa ba. Idan taron kasa ne, wacce doka ce ta kafa shi? Idan taron kasa ne, yaushe aka yi zaben wakilan? Idan taron kasa ne, ina matasa suke wadanda zasu karbi shugabancin gobe?" Yace cigaba da cewa "saboda haka shugaban kasa ne ya ga an matsa masa sai ya tara tsofaffi ya kaisu yana basu shayi da wuri mai sanyi ana kuma biyansu fansho ta bayan fagge. Wato yawancinsu suna fansho ne amma ba'a biyansu. Yanzu taron kasa ya biya bukatarsu."

Alhaji Aminu Adama na kungiyar matasa shiyar Kaduna, cewa yayi "an shirya taron ne kawai domin dagula hankulan 'yan Najeriya. Taro ne da gwamnati ta shirya domin ta wawantarwa jama'a hankula daga abubuwan da suka damesu kamar rashin zaman lafiya da talauci da yunwa."

Ga rahoton Isa Lawal Ikara
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG