Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Sami Nasara Karo Na 3 A Kotun Daukaka Karar Zaben Gwamna A Najeriya


Zaman Kotu
Zaman Kotu

Hukuncin kotun daukaka kararrakin zaben gwamna a jihar Filato da ke arewacin Najeria ya ba da adadin shari'un gwamnoni 3 kenan da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta sami nasara.

Kotun daukaka kararrakin zaben Najeriya da ke zama a Abuja ta soke nasarar da gwamnan jahar Filato Caleb Mutfwang na jami'iyyar PDP ya samu a zaben da ya gabata, tare da ayyana Nentawe Yilwatda na jami'iyyar APC a matsayin halataccen wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Hukuncin kotun na jihar Filato da ke arewacin Najeria ya ba da adadin shari'un gwamnoni 3 kenan da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta sami nasara a kotun daukaka kara kawo yanzu.

Idan za'a tuna, kotun daukaka karar da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da soke zaben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

A zaman yanke hukuncin da aka yi a ranar Juma'a 17 ga watan Nuwamba, kotun ta ayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Nasiru Yusuf Gawuna da Abba Kabir Yusuf
Nasiru Yusuf Gawuna da Abba Kabir Yusuf

Da ma can baya karamar kotun sauraren kararrakin zabe ce ta soma ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan da ta bayyana cewa akwai kuri’u marasa inganci da yawa da ta cire daga cikin kuri'un da aka kada wa Abba Yusuf.

To sai dai kuma Yusuf ya kalubalanci hukuncin kotun ta sauraron kararrakin zaben da ta soke nasarar da ya samu a kotun daukaka kara, wadda ita ma ta tabbatar da hukuncin karamar kotun.

A jihar Zamfara duk da yake gwamnan jihar Dauda Lawan Dare na jam'iyyar PDP ya sami nasara a karamar kotu, murna ta koma ciki a kotun daukaka kara.

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dan Takarar
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dan Takarar
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle

Yayin da Bello Matawalle, wanda yanzu haka shi ne karamin minista a ma'aikatar tsaro ya daukaka kara a babbar kotu ta gaba, kotun ta ce ta gamsu da hujjojin da ya bayar cewa hukumar zabe ta INEC ba ta hada da kuri'un wasu kananan hukumomi ba, wadanda shi Matawalle yake da'awar ya sami nasara.

Kananan hukumomi 3 ne lamarin ya shafa daga cikin kananan hukumomi 14 na jihar, da suka hada da Maradun, Birnin Magaji da Bukkuyum.

Kotun ta daukaka kara ta jingine ayyana Dauda Lawan Dare a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ta Zamfara, inda ta umarci hukumar zabe da sake gudanar da zabe a yankunan kananan hukumomin 3 da ko dai ba'a gudanar da zabe ba, ko kuma ba'a kyarga da kuri'unsu ba.

Gwamna na 3 kuma na baya-bayan nan shi ne gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang na jami'iyyar PDP, wanda shi ma ya yi nasara a shari'ar farko ta kotun sauraren kararrakin zabe.

Gwamnan Jihar FIlato Caleb Mutfwang
Gwamnan Jihar FIlato Caleb Mutfwang
To sai dai kuma lamarin ya sauya a kotun daukaka kararrakin zabe da ke zama a Abuja, wadda ta umurci hukumar zabe da ta kwace takardar shaidar lashe zaben gwamnan da ba shi, ta kuma mikawa Nentawe Yilwatda na jami'iyyar APC.
Kotun tace ta soke zaben gwamnan na jahar Filato ne bayan nazari da ta yi kan hujjojin da Nentawe Yilwatda ya gabatar a gabanta, na cewa jami'iyyar PDP ba ta da tsari na zababbun shugabannan jami'iyya kafin gudanar da zaɓe.
To sai dai da alama dukkan wadannan shari'un da ma wasu da dama da kotun daukaka kararrakin zaben ta gabatar, za su karkare ne a gaban kotun kolin kasar, wacce ita ce za ta zartar da hukunci na karshe.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG