Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na jam’iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
A ranar ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023 aka gudanar da zaben Gwamna a Najeriya, inda INEC ta ayyana Muhammad a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan, Sadique Abubakar ya shigar da kara a kotun sauraren kararrakin zabe.
Kotun ta jaddada nasarar Muhammad, lamarin da ya sa Abubakar ya garzaya kotun daukaka kara a Abuja.
Kotun mai Alkalai guda uku ta yi watsi da daukaka karar da dan takarar na jam’iyar APC ya yi a zaman da ta yi a ranar Juma’a.
Tun da misalin karfe takwas na safe lauyoyin masu shigar da kara dana kariya suka bayyana a kotun domin sauraron irin hukuncin da alkalan za su yanke.
Kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar dan takarar APC, Abubakar ya shigar saboba babu wata kwakkwarar hujja balle madogara kan zarge-zargen da ya yi.
A jawabinsa na bayyana godiya wa Allah dangane da nasarar da ya yi a karo na biyu, zabebben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammead Kauran Bauchi, ya mika hannun gayyata wa sauran ‘yan siyasan jihar Bauchi domin su zo a tafi tare don ciyar da jihar gaba.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:
Dandalin Mu Tattauna