Sai dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya kwantar da hankalin magoya bayansa.
Batun aringizon kuri’u da kasancewar gwamna Abba Kabir Yusuf sahihin dan Jam’iyyar NNPP ko akasin haka da kuma halaccin sanar da sakamakon hukuncin kotun ta kafar manhajar ZOOM ta intanet sune manyan al’amuran da suka mamaye mahawara tsakanin lauyoyin bangarorin biyu a yayin shari’ar.
Dr Kabiru Sa’idu Sufi, masanin kimiyyar siyasa ne dake koyar da wannan fanni a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano ya yi fashin baki. “Abubuwa manya da suka fi fitowa a wannan hukuncin sune ko dai-dai ne ko ba dai-dai ba ne a sanar da hukuncin kotu ta kafar intanet, wadda kotun ta tabbar da cewa, dai-dai ne. Sai batun sahihancin kasancewar shi gwamna a matsayin dan Jam’iyyar NNPP”.
Ana su bangaren masana shari’a da dokokin kasa, sun fayyace mataki na gaba da wadanda suka yi rashin nasara ka iya dauka. Barrister Ibrahim Chedi shine sakataren reshen jihar Kano na kungiyar lauyoyin Najeriya ya ce, “Yanzu abin da ya rage shine bangaren gwamna da Jam’iyyar NNPP su tafi kotun koli, wadda haka ne zai dakatar da rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin gwamnan Kano, sai dai idan kotun koli ta tabbatar dashi a kujerar gwamna, to lallai shi Abba Kabiru Yusuf zai sauka a tabbatar da Gawuna”.
Sabanin yadda aka yi hasashe, al’umar jihar Kano na ci gaba da harkokin su na yau da kullum bisa doka da oda kamar yadda suka saba. Amma Dr. Kabiru Sa’idu Sufi ya alakanta wannan nasara da wasu batutuwa. “Mutane da yawa suna da masaniyar cewa, hukuncin da kotun ta yanke ba shine karhse ba, sannan mutanen gari suna fama da kan su saboda kalubalen tsadar rayuwa, kana wasu ma na cewa, duk wadannan harkoki na siyasa ne daya shafi wasu shugabanni mutane biyu kawai, don haka bai kamata su dauki zafi akai ba”.
A jawabinsa ga al’umar jihar, a daren jiya gwamna Abba Kabiru Yusuf ya yi jan hankali game da muhimmancin zaman lafiya, yana mai nanata cewa, lauyoyin sa zasu daukaka kara zuwa kotun koli.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna