Bayan an bayyana sakamakon zaben jihar Rivers inda aka ce PDP ce ta ci zaben gwamnan jihar da kuri'u sama da miliyan daya yayin da da kyar APC ta samu kuri'u sama da dubu dari daya. Sakamakon zaben ya jawo korafe-korafe da dama. To amma tuni APC ta yi watsi da sakamakon zaben.
Kungiyoyin kasa da kasa da suka sa ido a zaben sun yi kira da a soke zaben jihar Rivers bayan abubuwan da suka yi la'akkari da su.
Hakazalika jam'iyyar APC ta ce ba ta yadda da sakamakon zaben jihar Akwa Ibom ba inda ta bukaci a soke zaben.
Yanzu haka dai ra'ayoyin 'yan jihar Rivers suna karo da juna akan zaben. Wani dan jihar ya ce nasarar da Wike na jam'iyyar PDP ya samu nufi ne na Allah.
Ya ce yawancin 'yan jihar suna murna da nasarar. Amma kuma wani dan jihar ya ce abubuwan da ya gani da idanunsa ba su yi kama da zaben gaskiya da adalci ba.
Idan muka duba jihar Imo lamarin ya sha banban. Duk da yake, kawo yanzu ba'a bayyana sakamakon zaben gwamna da na 'yan majalisar dokokin jihar ba 'yan jam'iyyar APC da PDP sun amince da soke sakamakon zaben wasu kananan hukumomi da hukumar zabe ta yi, saboda an kama wasu da suka yi aringizon kuri'u tare da hallaka rayuka.