Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obi Ya Lashe Imo, Abuja, Atiku Ya Kawo Sokoto


Manyan 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya
Manyan 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya

A ranar Asabar aka gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun dokokin tarayya a Najeriya

Hukumar zabe ta INEC, ta ayyana dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi, a matsayin wanda ya fi yawan kuri’u a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Obi (LP) – 352, 904

Tinubu (APC) – 66,171

Atiku (PDP) – 30, 004

Kwankwaso (NNPP) – 1,536

Kazalika Obi, ya lashe zaben shugaban kasa a Abuja, babban birnin Najeriya da gagarumar nasara.

Obi ya samu nasarar lashe kananan hukumomi hudu daga cikin shida da ke birnin, wadanda suka hada da Bwari, Kuje, Gwagwalada da AMAC.

Hukumar zabe ta INEC ta sanar cewa Obi ya samu kuri’a 281,717 yayin da APC ta samu kuri’a 90,912. Jam’iyyar PDP kuwa ta samu kuri’a 74,193 a zaben kamar yadda INEC ta sanar.

A gefe guda kuma, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Babban jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Kabiru Bala, wanda shi ne shugaban jami’ar ABU Zaria ne ya gabatar da sakamakon a ranar Talata.

Atiku ya samu kuri’a 288,679 yayin da Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 285,444.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG