Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
NIGERIA-ELECTION/ BOLA TINUBU
NIGERIA-ELECTION/ BOLA TINUBU

Bayan Zaben Shugaban Kasa Mai Cike Da Takaddama An Ayyana Tinubu Na A Matsayin Zababben Shugaban Kasar Najeriya

Da asubahin yau Laraba ne hukumar zaben Najeriya ta ayyana dan takarar jam'iyyar mai mulki ta APC, Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, bayan da aka gudanar da zaben a karshen mako cike da takaddama, yayin da manyan jam'iyyun adawa biyu suka yi watsi da sakamakon.

04:54 Maris 01, 2023

Bayan Zaben Shugaban Kasa Mai Cike Da Takaddama An Ayyana Tinubu A Matsayin Zababben Shugaban Kasar Najeriya

Da asubahin yau Laraba ne hukumar zaben Najeriya ta ayyana dan takarar jam'iyyar mai mulki ta APC, Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, bayan da aka gudanar da zaben a karshen mako cike da takaddama, yayin da manyan jam'iyyun adawa biyu suka yi watsi da sakamakon.

Nasarar da Tinubu ya samu ta kara wa jam’iyyar APC mai mulki karfin mulki a kasar da ke kan gaba wajen samar da man fetur a nahiyar Afirka, kuma mafi yawan al’umma, duk da cewa ya gaji dimbin matsaloli daga shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi ma na APC.

Tsohon gwamnan cibiyar kasuwanci ta Legas ya samu kuri’u miliyan 8.79, inda babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, ya samu kuri’u miliyan 6.98. Peter Obi, wani sabon shiga mai farin jini tsakanin matasa ya samu kuri’u miliyan 6.1.

Dokar zaben Najeriya ta ce dan takara zai iya yin nasara ne kawai ta hanyar samun kuri’u fiye da abokan hamayyarsa, matukar ya samu kashi 25% na kuri’un a akalla kashi biyu bisa uku na jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, wanda shi ma Tinubu ya yi nasarar yin hakan.

XS
SM
MD
LG