Ministan harkokin wajen kasar Nijar Kane Aichatou Boulama ce ta bayyana haka a wata hira da ta yi da wakilin Muryar Amurka Abdoulaziz Adili Toro, yayin da ta kawo wata ziyara anan Amurka.
“Amurka ta kama mana kwarai, ta kama mana bisa abinda ya shafi horo da kayan yaki da ba da bayanan sirri bisa abin da ya ke faruwa musamman bisa yakin da mu ke yi da Boko Haram.” In ji Boulama
Dangane da irin matakan da kasar ke dauka a gashin kanta wajen yaki da ta’addanci, Boulama ta ce shugaban kasar Mahamadou Issoufou na daukan matakan da suka da ce musamman abin da ya shafi hada kai da kasashen makwabta domin yaki da wannan matsala.
“Nijar da Najeriya da Chadi da Kamaru da ma Benin mun girka wata runduna ta musamman domin yaki da kungiyar da ake kira Boko Haram.
Ta kara da cewa duk da ana samun karin hare-hare, ya kamata a ci gaba da nunawa dakarun kasar goyon baya da kuma jinjinawa saboda irin na mijin kokarin da suke yi.
Ga cikakkiyar hirar da Muryar Amurka Ta Yi Da Minista Kane Aichatou Boulama: