Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGER REPUBLIC: Malaman Addinai Sun Kira a Gudanar da Zaben Kasar Cikin Zaman Lafiya


 shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar
shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Daidai lokacin da shugaban kasar ya yiwa majalisar zartaswar kasar garambawul malaman addinin isalama da na kirista kira suka yi a gudanar da zaben kasar cikin zaman lafiya.

Malaman addinan biyu sun kira 'yan siyasa da shugabanni su tabbatar an dauki matakan ganin an gudanar da zabukan gamagari da kasar zata yi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Malam Salisu na Malam Atta na kwanar mutuwa cewa ya yi da zara an yi zabe to a tabbatar an ba nasara ga duk wanda Allah ya ba galaba,kada a sauya sakamako. Shugabanni su kiyaye adalci domin shi ne zai tabbatar da zaman lafiya. A ja kunnuwan wadanda zasu gudanar zabe su yi adalci.

Shi ma limamin babban cocin asembli Aliyu Yari kira yayi a tabbatar an yi zabe cikin kwanciyar hankali da tsanaki. Fatansu shi ne a fara zabukan lafiya a kuma kare lafiya. Duk wanda Allah ya ba a bashi kuma Allah ya tayashi rikon amana. Wadanda suka rasa kuma Allah ya basu ikon rungumar kaddara. Su kasance cikin hakuri a yi tafiya dasu.

Kamar malaman addinin musulunci su ma na kirista zasu cigaba da tallafawa wurin yin addu'o'i. Wadanda Allah zai zaba ya basu ikon yin adalci saboda salama ta tabbata a cikin kasar.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG