Ministan wanda kuma shi ne kakakin gwamnatin Nijar ya bayyana dalilan kirkiro da ranar.
Gwamnati ta kirkiro da ranar ne saboda fadakar da al'umma akan yadda wannan lamarin safarar mutane ke kara yin kamari duk da matakan da aka dauka da koma kokarin dakileta nan da can..
Yace ana cigaba da samun mutanen dake yin anfani da talaucin wasu suna safararsu. Yace maza da mata da yara ne suke fadawa hannun masu safarar. Suna safararsu ko a kasarsu ta haihuwa ko kuma su kaisu kasashen ketare. Yace kasar Nijar bata tsira ba.
Inji ministan, kasar Nijar ta kuduri aniyarta a zahiri wajen yakar safarar mutane musamman idan aka yi la'akari da wata doka ta shekarar 2010 da ta haramta safara mutane.
Bugu da kari gwamnatin Nijar ta kafa wata hukuma ta musamman domin yaki da wannan muguwar sana'a a shekarar 2011.
Muhammad Al-Mansour na wata kungiya dake yaki da lamuran bauta a Nijar yace babu komi da aka yi domin an kafa doka ne kawai tare da kafa hukuma ba tare da basu kayan aiki ba. Hukumar a Niamey kawai take kuma basu da motoci da zasu shiga cikin kasar su ga abun dake faruwa.Har yanzu ana safarar mutane a cikin kasar.
Kasar Nijar ta yi kamarin suna a safarar mutane. A shekarar 2013 an samu gawarwakin mutane 92 wadanda suka rasa rayukansu a kokarin da suka yi na tsallakawa kasar Algeria ta hanyar hamadar sahara. A wannan watan ma hukumomin Nijar sun samu nasarar cafke wata mata 'yar Najeriya wacce ta yi ruwa da tsaki wajen safarar 'yan mata biyu su ma 'yan Najeriya zuwa kasar Mali inda ta tilasta masu yin karuwanci.
Garahoton Yusuf Abdullahi.