Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shagulgulan Maulidi A Najeriya


Wasu da suka halarci taron Maulidi a birnin Jos a jihar Filato (Hoto: Facebook/Bashir Muktar/Bashcology)
Wasu da suka halarci taron Maulidi a birnin Jos a jihar Filato (Hoto: Facebook/Bashir Muktar/Bashcology)

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya daukacin al’umar Musulmi murnar zagayowar wannan rana.

Musulmai da dama a sassan duniya na shagulgulan bikin Maulidi don murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammad S.A.W.

Eid-ul-Maulud biki ne da Musulmi ke yi a duk shekara don nuna murna ga zagoyar wannan rana.

Mutane da dama musamman yara kanana da mata, kan dinka sabbin kayayyaki yayin da ‘yan makaranta kan yi jerin gwano a wasu birane don marabtar wannan rana.

Bikin na Maulidi har ila yau na dauke da tarukan wa’azi, addu’o’i da gudanar da kasidun yabon Manzon Allah S.A.W.

Hukumomin Najeriya sun ayyana Talata a ranar hutu domin a ba masu wannan biki damar yin shagulgula.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya daukacin al’umar Musulmi murnar zagayowar wannan rana.

“Ina mai matukar farin cikin mika sakon taya murna na zaman lafiya, hadin kai da fatan alheri ga al’umar Musulmi, ‘yan kasa da Musulmi a duk fadin duniya yayin da suke wannan biki na Eid-ul-Maulud.”

Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da wannan rana, wajen yin bayani ga ‘yan kasa kan ayyukan da jami’an tsaron kasar ke yi a kokarin magance matsalar tsaro da ta addabi kasar.

“Samun karin hadin kai daga al’umar kasa, da daukan matakai daban-daban, da kuma zaburar da ‘yan sandanmu, jami’an tsaro da shugabannin dakarunmu, na taimakawa gwamnati wajen samun nasarori akan masu aikata ayyukan ta’addanci.” Buhari ya ce cikin sanarwar wacce kakakinsa Garba Shehu ya fitar.

Buhari ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da su duba irin rahotannin da suke aikawa kan sha’anin tsaro duba da cewa wasu rahotannin za su iya yin mummunan tasiri ga muradun da aka saka a gaba.

Rahotanni na cewa a tsaurara matakan tsaro a wasu biranen Najeriya yayin da al’umar Musulmin ke gudanar da bukukuwan na Maulidi.

XS
SM
MD
LG