Amma Ministar Kudi da Tsare-tsare Zainab Shamsunah Ahmed ta bayyana mana cewa hauhawan farashin kayan abinci na cikin abubuwan da ke tayar wa Shugaba Muhammadu Buhari da hankali.
Kayan abinci ya yi tsada a kasuwannin Najeriya musamman ma a babban birnin tarayya Abuja. Duk sanda mutum ya ziyarci kasuwa, zai iya gama yawo ya dawo, ba tare da ya sayi wani abu ba, saboda yadda farashin kayaiyaki suka tashi, musamman ma kayan miya.
Wani dan kasuwa Malam Mohammed mai sayar da kayan miya a kasuwar Area 11 dake babban birnin tarayya Abuja ya ce yana sayar da tumatur a kwandon roba madaidaici wanda aka fi sani da kwandon bola, Naira dubu 4,000, attaragu kuma Naira dubu 3,500, haka ma tattasai. Amma abinda aka samu saukin sa shi ne albasa, wanda ake sayar dashi Naira 1,500.
Malam Mohammed ya ce an samu saukin irin su dankalin turawa wanda a yanzu ana sayar da kwandon roba 2,000 daga 4,000 sannan dankalin hausa kuma Naira 1,000 daga 1,500 saboda an fara samun sabon dankalin turawa yanzu a kasuwa.
Karin bayani akan: Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Naira, Godwin Emefiele, Shugaba Muhammadu Buhari, Zainab Shamsunah Ahmed, Abuja, Nigeria, da Najeriya.
Akan haka muka gana da Ministar Kudi da Tsare-tsare don jin ko suna sane da kokekoken mutane a game da hauhawan farashin kayan abinci.
Minista Zainab Shamsunah Ahmed ta ce harkar tsaro da kuma ta hauhawar farashin kayan abinci su ne abubuwa biyu da ke tayar wa Shugaba Muhammadu Buhari da hankali, kuma tuni ya baiwa Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele da kuma ita kanta umurnin samo hanyar tallafawa marasa karfi.
Zainab Ahmed ta kara da cewa an riga an fara abinda ake kira Conditional Cash Transfer Ko CCT kuma har an riga an ba gidaje miliyan 6 wanda Naira 5,000 in aka kirga mutane 6 a gida daya so miliyan 6 ya kama mutane miliyan 36 kenan. Kuma har ila yau ana kan bayar wa ba za a fasa ba.
Daya cikin kayan abinci da farashin sa ya bamu mamaki shi ne shinkafa, wadda a yanzu ake ce mata Hajiya Babba saboda kudin ta ya ki sauka tun farkon kafa wannan Gwamnati da aka rufe kan iyaka.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda: